Rukunin farko na alhazai daga ƙasashen waje ya sauka a Madina bayan gabatar da aikin Ummara

0
472

 

A ranar Litinin ne rukunin farko na alhazai ƴan ƙasashen waje ya sauka a Madina bayan gabatar da aikin Ummara.
Rukunin alhazai 37 ne da suka zo daga Pakistan.
Ziyarar alhazan zuwa masallacin ma’aiki za ta gudana ne a bisa ranar da aka sanya ta hanyar amfani da manhajar Eatmarnah da kuma amfani da hanyoyin kariya daga kamuwa da cutuka.
Kamar yadda tsare-tsare na ma’aikatun ƙasar Saudi Arebiya suka kasance, alhazan Ummara 20,000 ne za su riƙa kai ziyara kabarin ma’aiki a rana, mutane 60,000 za  su yi sallah a rana.
Hakan kuma rukuni na uku na alhazan Ummara daga Indonesiya ya sauka a Makka a ranar Litinin domin gudanar da ayyukan Ummara a masallacin haraji na Makka.
Daga saukar su a ka gudanar da tsare-tsare na kariya daga kamuwa da cutuka, inda a ka killace su na tsawon kwanaki uku kafin su fara ibadar Ummara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here