Hukumar Jin daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Borno ta fara karɓar N1,000,000 a matsayin kuɗin ajiya daga maniyyata na aikin Hajji 2021.
Hakan ya zo ne a bisa umarnin da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta baiwa hukumomi da ma’aikatun kula da aikin Hajji a ɗaukacin jihohin ƙasar nan.
Wannan naira miliyan ɗaya (N,1000,000) za a ajiye ta ne kafin kuma NAHCON ta ƙayyade farashin zuwa Hakkin 2021 nan gaba.
A wata sanarwa da Shugaban Hukumar Jin daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar, Alhaji Ali Mallam Bukar ya fitar ranar Laraba ta ce, maniyyatan da suke da buƙata za su iya biyan kuɗin a tsitstsinke ta hanyar sabon shirin nan na Fashin Gata na Zuwa Hajji a bankin Jaiz a watan Oktobar bana.
Shugaban ya ƙara da cewa hukumar za ta bawa tsarin nan na kulawa da wanda ya fara zuwa muhimmanci sosai domin baiwa maniyyatan da suka biya kuɗin Hajji 2020 amma suka yanke shawarar cigaba da ajiye wa domin Hajjin 2021 cikakkiyar dama a kan waɗanda suka biya na Hajjin bana.
Sanarwar, wacce shugaban ya sanyawa hannu ta yi kira ga maniyyatan da suka biya kuɗin ajiya na zuwa Hajjin 2020 da su yi sauri su cikashe ƙuɗaɗen da gaggawa.
Hukumar ta kuma yi kira ga maniyyatan da su biya kuɗin ta banki da kuma fito da shaidar biyan kuɗi mai ɗauke da suna, lambar waya da kuma lambar fasfo a bayan takardar shaidar biya zuwa hukumar.
Haka zalika hukumar ta gargaɗi maniyyatan da su yi hankali da waɗanda za su yi musu gada ta biyan kuɗin da sunan hukumar, inda ya bayyana cewa hukumar ba za ta ɗauki asara ba idan aka biya kuɗi ta hannun wanda bata san da shi ba