Kwamitin Adashin Gata na Hajji ya miƙa rahoto ga shugaban NAHCON

0
10

  

 

 

Daga Mustapha Adamu

 

Kwamitin da a ka kafa domin tabbatar da cigaban sabon tsarin nan mai taken Adashin Gata na Hajji (HSS) ya miƙa tahotonsa ga Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Barista Zikrullah Kunle Hassan.

 

Sanarwa da Shugabar Fannin Hulɗar Jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, ta ce kwamitin ya ƙunshi wakilan shugabannin Hukumomin Jin Daɗi da Walwalar Alhazai na jihohi da na shugabannin gudanarwa na NAHCON.

 

Bayan da shugaban kwamitin, Alhaji Usman Shamaki ya gabatar da rahoton, shugabannin Hukumomin Jin Daɗi da Walwalar Alhazai na jihohin, a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar tasu kuma shugaban hukumar Hajji ta Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar S. Pawa Dembo, da kuma jami’an NAHCON, sun tattauna a kan sakamakon rahoton sannan suka fitar da matsaya.

 

Abubuwan da a ka tattauna sun haɗa da tsare-tsaren yin rijista, buɗe sashi-sashin Adashin Gata na Hajji a hukumomin Hajji na jihohi, tsarin raba kuɗaɗen shiga, wayar da kai a kan shirin, haɗin gwiwar hukumomin Hajji na jihohi da Jaiz a kan manhajar shirin na HSS da kuma wa’adin zuba hannun jari da ke da alaƙa da ranar arfa.

 

A ƙarshen taron, shugaban ƙungiyar shugabannin Hukumomin Hajji na jihohi ya yabawa shugaban NAHCON a bisa tsarin jagorancin sa na tafiya da kowa, inda ya kuma yi kira ga ƴan ƙungiyar da su gaggauta tabbatarwa shirin ya aiwatu a jihohin su.

 

A nashi jawabin, Alhaji Zikrullah, godewa ɗaukacin ƴan kwamitin a bisa ƙwazon da suka yi, inda yayi kira a gare su da su ƙara dagewa wajen bunƙasa harkar aikin hajji a jihohin su.

 

Ya kuma tunatar da su ce tun kafin a haifi kowa a wajen taron ake gudanar da aikin Hajji haka kuma za a cigaba da gudanar da shi bayan ba su, inda ya yi kira ga kowa da ya zage dantse wajen bunƙasa harkar

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here