Babban Ofishin Kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya samar da wata manhaja mai suna “tanaqqul” domin alhazai su ajiye guraben motoci masu amfani da lantarki ta wayar salula domin amfani da motocin wajen yin ɗawafi da kuma sa’ayi a Safa da Marwa a masallacin Harami na Makkah.
Manhajar ta bada damar ajiye gurbin karɓar motocin ga masu buƙata da kuma rage cunkoso wajen biya a ta hannu a karɓi tikitin hawa motocin da kuma maida su, inda sabon tsarin ya samar da nasarar tabbatar da tsarin nan na tazara tsakanin alhazai.
Manhajar ta bawa alhazan damar biyan kuɗin hayar motocin ta yanar gizo ko biyan kuɗin a hannu bayan karɓar motar, inda ake biyan a tsawon awanni 24.
Domin karɓar hayar motocin ta manhajar,ana buƙatar suna, katin shaidar zama ɗan ƙasa, adreshin Alhaji da kuma lambar waya.
Duk wanda ya nemi karɓar hayar motar ta yanar gizo zai samu saƙo ta waya domin tabbatarwa, inda zai faɗi rana, lokacin da yake da buƙatar motar da kuma sunan sa.
Kawo yanzu dai mutane 2,000 suka amfana da manhajar.