A ƙalla gurare 60,000 ne za a samar da na’urar WiFi kyauta a guraren al’umma a faɗin ƙasar Saudi Arebiya a wani ɓangare na tsarin Sadarwa da Fasaha mai taken (CITC).
Asibitoci, manyan kantuna, guraren fakin ɗin ababan hawa da kuma Masallatan Harami Guda biyu na daga cikin mahallan da za a samar da na’urar WiFi ɗin kyauta, kamfanin dillancin labarai na Saudiya ya rawaito ranar Lahadi.
Sabon tsarin ya kuma haɗa da samun haɗa na’urar WiFi ɗin ta jama’a ga duk wani kamfanin sadarwa har na tsawon awanni biyu a kowacce rana a birane da dama na ƙasar Saudiyya.
CITC ɗin ta haɗa gwiwa da kamfanunuwan samar da sadarwa ta tarho domin ƙirkiro wannan hanyar kuma za ta ci gaba da kula da aikin har zuwa a kammala shi.