Ummara: Sama da ma’aikatan sa kai 300 ne suke hidima a babban masallacin Makka

0
6

 

 

 

Sama da mutane 300, da suka haɗa da likitoci, injiniyoyi da sauran ma’aikatan lafiya ne ke bada agajin gaggawa da kuma wayar da kai ga alhazan Ummara game da kariya daga yaɗuwar cutar corona, da suka haɗa da samar da tazara ga juna da kuma saka takunkumin fuska.

 

 

 

Wata Ƙungiyar Taimako mai suna Saudi Red Crescent Authority (SRCA) ce ta tabbatar da cewa ɗumbin mutane ne suka nuna buƙatar su ta yin hidima a Masallacin Harami na Makkah, kuma suna alla-alla su yiwa alhazai hidima lokacin da aka buɗe Ummara bayan an samu tsaiko sakamakon annibar COVID-19.

 

 

 

Amma kuma sai a ka ɗauki adadi ƙanƙani saboda tabbatar da tsarin tazara da kuma kariyar alhazai daga kamuwa da cutar corona.

 

 

 

Jami’in Ayyukan Sa kai a SRCA a Makkah, Hanaa Al-Shamrani ya shaidawa Arab News cewa, a makon farko na buɗe Ummara, ƴan aikin sa kan sun ƙagu su yiwa alhazai hidima.

 

 

 

“Mun karɓi takardun neman yin aikin sa kan da dama daga mutane daga birane daban-daban na faɗin Saudiyya ba tare da zaɓe ba. Amma duba da yanayin da a ke ciki, SRCA ta karɓi takardun ne na iya Makkah domin domin a yi aiki mai inganci wanda yayi daidai da matakan kariya da aka sharɗanta, ” in jishi.

 

 

 

Ya ƙara da cewa ƴan aikin sa kan sun iya yaruka da suka haɗa da yaren Urdu, turanci, Turkiya da sauran yarurruka da suka koya sakamakon mu’amala da suke yi da alhazai a yayin Hajji da Ummara a Makkah.

 

 

 

 

“Ƴan aikin sa kan za su riƙa lura da masu ciwon suga, hawa jini, kana da waɗanda zafin gari da rana su ke galabaitar da su da kuma waɗanda suka ji wasu ƙananan ciwuka,” in ji Al-Shamrani.

 

 

” Su ƴan sa kan suna kula da waɗan nan masu rashin lafiyar ne ta hanyar ƙwarewa, inda kuma idan ciwon ya ta’azzara, sai mu miƙa mutum zuwa asibiti mafi kusa,”

 

 

 

Ta kuma ƙara da cewa kafin ɓulkar annobar corona, ma’aikatan sa kai na raba kyaututtuka ga alhazai da suka haɗa da carbi, dardumar sallah da kuma kayan ciye-ciye, amma a bana ba zai yiwu ba saboda annobar.

 

 

 

Mai magana da yawun SRCA ɗin, Abdul Aziz Badamoan ya faɗawa Arab News cewa rukunin ma’aikatan sa kan na hukumar sun fara aiki ne a maslacci mai tsarki ranar Juma’a a gurabe huɗu, kuma mata 20 ne maza 26.

 

 

 

” Ƴan sa kan na yin hidima ne a kowacce kusurwa ta masallacin, inda ya haɗa da da farfajiyoyi da guraben sallah na ɓangaren mata a masallacin,” in ji shi

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here