Hukumar kula da Jin daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Sokoto ta ce tana daf da fara amfani da sabon tsarin nan na Adashin Gata na Hajji a jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Shehu Muhammed Dange ne ya bayyana hakan lokacin da ga tarbi tawogar Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta yankin.
Dange ya bayyana cewa hukumar ta fara yunƙurin samar da sashin da zai riƙa gudanar da tsarin a shalkwatar hukumar kamar yadda NAHCON ta bada umarni.
Jagoran tawogar, Alhaji Alh.Umar Garba Kyadawa, wanda shine Kwamishinan NAHCON mai kula da yankin Arewa maso Yamma, ya ce sun zo jihar ne domin ganin shirin da hukumar ke yi wajen aiwatar da tsarin Adashin Gata na Hajji da kuma duba wasu ayyukan cigaba da NAHCON ke yi a jihar.
Kwamishinan yankin ya samu rakiyar wakilin yankin Sokoto, Alhaji Isma’ila Gambo da mataimakin sa, Alhaji Garba Yakubu, da sauran ƴan tawogar