NAHCON ta buɗe sabon sashin na yaƙi da zamba

0
542

 

 

 

Hukumar kula da Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ƙaddamar da sabon sashi na yaƙi da zamba da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana a ranar Alhamis, inda ta rantsar da ma’aikatan sashin.

 

 

 

Shugaban hukumar, Zikrullah Kunle Hassan ne ya ƙaddamar da sashin a ofishin hukumar a gaban Mataimakin Kwamishina kuma Shugaban sashin sa ido da bincike, Kufolati Kayode, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar Daƙile Aikata Cin hanci da Rashawa, Farfesa Bolaji Owasanoye.

 

 

 

Hajj Reporters ta fahimci cewa rantsar da ma’aikatan sashen ya tabbatar da yunƙurin samar da wani ɓangare da zai riƙa kula da kuma cusa aƙidar yin gaskiya a harkar hajji a Nijeriya.

 

 

 

Wannan jaridar ta tuna cewa an bawa shugabancin NAHCON da ya gabata sahalewar ƙirƙiro da sashen daƙile zamba, amma bai iya cimma aiwatarwa ba kafin barin kujerar shugabancin.

 

 

Tsarin shine a ƙirƙiro da fannin, mai ɗauke da jami’ai daga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, wato EFCC, ICPC, DSS, NIA da ƴan sanda domin su ƙarfafa sashin.

 

 

 

Ana tsammanin sashen ya fara aiki da gaggawa bayan an rantsar da ma’aikatan sashin


 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here