COVID-19: Masu harkar Hajji da Ummara na tsananin buƙatar tallafi

0
16

 

Masu harkokin jigilar Hajji da Ummara sun koka a kan cewa suna tsananin buƙatar tallafi daga gwamnatin tarayya domin su samu su cigaba da harkokinsu da suka saba.

Ƙungiyar Masu Harkokin Hajji da Ummara (AHOUN) ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa sun samu gagarumar asara sakamakon soke Hajji da Ummara na bana da a ka yi saboda annobar COVID-19, wacce a ka fi sani da korona.

Sun roƙi gwamnatin tarayya da suma ta basu tallafin kuɗaɗe kamar yadda ta yiwa sauran ɓangarori da illar annobar ta shafa.

” Muna miƙa koken mu ga gwamnatin tarayya domin AHOUN ta fi kowanne ɓangare shan wahala. Ba a yi aikin hajji a bana ba kuma hakan ya shafi harkokin mu da duk al’amuran mu na rayuwa,” Darakta a Kamfanin Jigilar Tafiye-tafiyen Jirgin Sama na Hasha ya shaidawa Daily Trust.

Shi kuwa Shugaban Kamfanin Sufurin Jirgin Sama na Comerel Travels, Ustaz Abubakr Siddeeq Muhammad cewa yayi annobar ta zo ne lokacin da canjin kuɗaɗen ƙasashen waje yayi tashin Gwauron zabi a 2019, lamarin da ya haifar da rashin ciniki a harkar.

Ya ƙara da cewa suna biyan hukumomi kuɗaɗen ayyukan su ne da dalar Amurka da riyal ta Saudi Arebiya.

Idan a ka kwatanta da shekarun baya, an samu ƙarancin matafiya yin Ummara a 2018 da 2019 a Nijeriya, inda maniyyata da dama suka fasa tafiyar duk da cewa sun yanki biza.

“Saboda tashin gwauron zabi da canjin kuɗaɗen ƙasashen waje yayi inda hakan ya kashewa mutane gwiwa idan suka ga irin maƙudan kuɗaɗen da za su kashe bayan sun lissafa zuwa naira,”  ya ce.

Ya ƙara da cewa babu laifi idan gwamnatin tarayya ta basu tallafin kuɗaɗe domin hakan alheri ne ga ƙasa baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here