Babban Ofishin Kula da Babban Masallaci Mai tsarki da Masallacin Ma’aiki na gagarumin ƙoƙarin feshin maganin kashe ƙwayoyin cututtuka da na turare a babban masallacin da kewayen sa inda aka yi ƙiyasin girman farfajiyar ya kai murabba’in miliyan ɗaya.
Ofishin ya samar da ma’aikatan tsafta 4,000 waɗanda suke aiki ba dare ba rana a salon karɓa-karɓa sau huɗu a rana.
Minti 35 kacal ake yi a yi feshin maganin kashe ƙwayoyin cututtukan a ɗaukacin masallacin Harami.
Rukunin ma’aikata tara ne, da suka haɗa da jami’an sa ido guda biyu a kowanne rukuni ne suke aiki feshin da tsaftace babban masallacin