Indonesia ta kafa sharuɗɗa uku kan Hajjin 2021

0
391

 

Hukumar Kula da Harkokin Addinai ta Indonesiya ta kafa wasu sharuɗɗa guda uku a kan Hajjin 2021, waɗanda suka zo daidai da tsare-tsaren Hajjin bana.

 

Shugaban hukumar, Nizar ya ce a sharaɗi na farko, za a tura duka adadin guraben alhazan da aka bawa ƙasar amma fa da sharaɗɗi.

 

” Hakan zai faru ne kaɗai idan annobar COVID-19 ta tafi ko kuma na samu rigakafin cutar,” in ji shi a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Asabar.

 

Na gaba kuma shine rage yawan alhazan da za su je Hajjin da kashi 30 ko 50 kuma hakan ma za a yi ne a ƙarƙashin sharuɗɗan kariya daga kamuwa da cututtuka.

 

Sharaɗi na ƙarshe shine za a iya sake soke zuwa aikin Hajjin idan Saudi Arebiya ta kuma hana ƙasashen waje zuwa.

 

Nizar ya ƙara nanatawa cewa gwamnatin Indonesiya ta soke zuwa aikin Hajjin 2020 ne saboda kariya da tsaron alhazanta daga kamuwa da cutar COVID-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here