‘Yan Arewa Ku Bar Bacci, Ku Farka Ku Kare Kawunanku Daga Kisan Wulakancin Da Ake Yi Maku!

0
5

 

Daga Imam Murtadha Gusau

 

 

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

 

Assalamu Alaikum

 

Wallahi, tun ranar da aka yiwa bayin Allah, ‘yan uwan mu yankan rago a jihar Borno, Allah ya sani, na kasa yin bacci, na kasa cin abinci, ba domin komai ba sai don irin damuwa da bakin cikin da na samu kai na a ciki!

 

Tun ranar da aka sace bayin Allah a jihar Zamfara, suna Sallah, tare da limamin su, na rasa fahimtar kai na! Duk hare-haren da ‘yan ta’adda suke kai wa a jihar Zamfara da sauran wurare a Najeriya, yana nema ya shigar da ni wata irin damuwa da ban taba shiga ba a rayuwata!

 

Kullun idan naji labarin cewa an sace bayin Allah a hanyar Kaduna zuwa Abuja, ko kuma wani yanki daga yankunan arewa, ko wani wuri a duk fadin Najeriya, ko an kai wa wasu bayin Allah hari, wadanda basu ji ba basu gani ba, ni kan dimauta, in fita hayyaci na gaba daya.

 

An sace ‘yar uwa ta, sai da aka biya kudi kafin a sake ta. An sace ‘ya ‘yan wani malami abokina su uku, sai da aka biya kudi kafin a sake su. Kai Allah ne kadai yasan iyakar bayin Allah da ake sacewa kullu yaumin a arewacin Najeriya. Allah ne kadai yasan bayin Allah da aka kashe ta wannan hanya, saboda watakila ‘yan uwansu sun kasa biyan kudin fansar ‘yan uwansu!

 

Anan Okene, Jihar Kogi, ‘yan ta’adda, masu satar mutane domin neman kudin fansa, sun addabe mu. Kullun daga a sace wannan, sai a sace wannan!

 

Hasbunallahu wa Ni’imal wakil!

 

Jama’ah, wai ace Dan Adam, musamman Dan arewacin Najeriya, ya zama ba bakin komai ba. A kashe shi a kashe banza, a yanka shi a yanka banza, aci mutuncinshi aci mutuncin banza. Baya da gata, baya da mai taimako?

 

Talakan arewa a halin yanzu ya zama baya da wani gata sai Allah da ya halicce shi?

 

Kowa ya sani, tsakani da Allah, wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari talakawa ne suka zabe ta. Kuma Allah shaida ne cewa mun yi mata addu’o’i, kuma muna ma kan yi. Sannan duniya shaida ce akan cewa mun yi masu uzuri, iya uzuri. Mun kyautata masu zato. Mun sa ido mu gani ko zasu ji tsoron Allah su gyara. To amma daga karshe, mun gano cewa, in dai har akan harkar arewa ne da ‘yan arewa ne, to babu abunda zasu yi na gyara. Domin su sun dauka cewa, dole ne ‘yan arewa su bisu, saboda irin son su da ake yi.

 

Sai gashi wai don rashin kunya da rashin imani, da rashin tausayi, da rashin tsoron Allah, wai Malam Garba Shehu, ya fito yana fadawa duniya cewa, wadannan manoman da aka yiwa yankan rago a jihar Borno, sunyi laifi, domin ba su ma nemi izinin gwamnati, domin yin noma a wannan wurin ba!

 

Yanzu don Allah, gwamnatin da ke ikirarin cewa ita gwamnatin talakawa ce, zata fadi haka? Yanzu domin Allah, akwai wani mutum Dan arewa, da zai taba yin tunanin cewa wannan gwamnati zata fadi haka akan wadannan bayin Allah, talakawa, wadanda ke neman abun da za su ci?

 

Allah wadaran naka ya lalace….

 

Kuma Allah ya isa… Allah ya isa… Allah ya isa!

 

Mu dai Allah ya sani, mun fito fili muna Allah wadarai, kuma muna masu yin Allah ya isa, akan duk wanda ya yaudare mu, kuma yayi muna dadin baki, har wannan gwamnati ta kafu!

 

Kuma ina mai shaida wa dukkanin ‘yan uwana ‘yan arewa cewa, wallahi wannan gwamnatin ba ta da wani amfani a gare mu! Kuma ba ta da wata kyakkyawar manufa ta alheri akan mu. Don haka ya zama dole, kuma ya zama wajibi, mu farka daga baccin da muke yi, mu fara nemar wa kawunanmu mafita daga wannan bakin mulki, mulkin fir’aunanci! Mulkin da baya amfanar da bayin Allah sai cutar da su. Idan kuma mun ki ji, to ya rage namu! Allah shaida ne akan cewa mun fada maku gaskiya, tsakaninmu da Allah!

 

Haba jama’ah, ace yau an wayi gari, duk wani Dan arewa baya cikin kwanciyar hankali. Ga rashin kwanciyar hankali saboda talauci, yunwa da tsadar rayuwa. Sannan ga rashin kwanciyar hankali saboda rashin tsaro. To da wane zamu ji? A kan hanya babu kwanciyar hankali. A gidan ka babu kwanciyar hankali. Kai a ko’ina Dan arewa baya cikin kwanciyar hankali!

 

Don girman Allah mu tambayi kawunan mu, kuma mu fadi gaskiya tsakanin mu da Allah, kar mu zama munafukai! Shin don Allah, misali, da ace Dan kudu ne yake mulkin Najeriya ayau, kuma wadannan abubuwa suke faruwa a arewa, don Allah me zamu ce? Don Allah me zamu fada? Shin don girman Allah shiru zamu yi ne? Ba zaka ji mun cika mimbarorin masallatai da coci-cocin arewa, da majalisun siyasar mu, da jaridun mu, da dukkan kafafen yada labarai, wurin yin Allah waddai da shi ba, da kuma mulkinsa?

 

To idan amsar ita ce haka ne, to me yasa muka yi shiru yanzu? Munafukai muke son zama ne? Mun zama idan namu yana kai, sai mu rinka kawar da kai daga duk barnar da ake yi, kawai saboda shi Dan arewa ne, ko don shi Musulmi ne, sai muce ayi shiru, a daina magana, saboda namu ne? Amma idan wasu suna kai sai ya zamanto ba haka ba? Haba jama’ah, don Allah wannan ba mummunan laifi bane a wurin Allah? Shin kuna nufin Allah ba zai kama mu saboda wannan rashin adalcin ba? Don Allah bari in tambaye ku, shin don girman Allah, da ace Annabi Muhammad (SAW) yana raye, shin zai yadda da wannan fuska biyun?

 

Wallahi ya zama dole, kuma wajibi mu farka daga baccin da muke yi. Mu sani, bamu da wurin da ya wuce arewa. Sannan Najeriya dai kasar mu ce. Da Musulmi da Kirista, da Dan arewa, da Dan kudu, duk wanda yayi laifi, sunan sa laifi. Haka duk wanda yayi daidai, to shima sunan sa daidai. Idan mun zama adilai, sai Allah ya taimake mu, amma idan mun zama munafukai, to zamu ci gaba da jin jiki wallahi, domin shi Allah babu ruwanshi!

 

Ina mai yi maku rantsuwa da Allah, yadda wadannan ‘yan siyasar suke zaluntar mu ayau, Allah ba zai taba barin su ba! Yadda wannan gwamnati ta dauke mu ba bakin komai ba, Allah ba zai bar ta ba. Jinin ‘yan arewa da ya zama ba bakin komai ba a wurinsu, ba zai taba tafiya a banza ba da izinin Allah? An wayi gari rayuwar mu ta zama banza a wurin wadannan mutanen? Ya Allah, bamu da karfi, ya Allah, kai ne kadai mai karfi, ya Allah, bamu da wani wayo, ya Allah, bamu da wata dabara, ya Allah, bamu da wani iko, mun kawo karar duk mai zaluntar mu gare ka, ya Allah, gasu nan gare ka, ya Allah, fir’auna da rundunarsa sun yayyanka bayin ka, daga karshe ka kama su, ya Allah… Ya Allah… Ya Allah, Ka kama duk wani azzalumi da yake kashe bayin ka, ya Allah, ka damki duk wanda yake cutar da bayin ka, irin yadda ka damki azzalumi irin fir’auna!

 

Ina malamai suke ne, ina sarakuna suke ne, ina jagororin arewa suke ne, ina ‘yan kasuwar arewa suke ne, ina masu kudin arewa suke ne, ina talakawan arewa suke ne, ina jami’an tsaron arewa suke ne, ina ‘yan jaridar mu na arewa suke ne, kai ina dukkanin ‘yan arewa suke ne! Wallahi, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, wallahi duk wanda yayi shiru akan wannan lamari na rashin tsaro da kisan gilla da ake yiwa ‘yan uwan mu, bayin Allah, a arewa, to tabbas ya zama munafuki! Kuma wallahi duk wanda bai yi Allah waddai da wannan bakin mulkin ba wallahi shima azzalumi ne, kuma macuci ne, mai ha’intar al’ummarsa.

 

Kuma ina mai yi maku rantsuwa da Allah, idan kuka ci gaba da yin shiru, to bala’in da Allah zai saukar a kan ku da zuri’arku, sai yafi wannan! Haba jama’ah!

 

Ina munafukan malamai suke, ‘yan cuwa-cuwa, shedanu, ‘yan 419, wadanda suka yaudari talakawan arewa da sunan addini? Ina kuke ya ku munafukai! Shin ba kune kuka ce a zabi wannan gwamnati ba? Ba kune kuka yi muna dadin baki ba? Shin ba kune kuka yi masu kamfen ba? To ta yaya ana yanka mu, yankan rago, amma kuma kunyi shiru? Ta yaya ana cin mutuncin mu baku ce komai ba? Ta yaya ana yiwa matayen mu fyade amma kun kama bakunan ku kunyi shiru? Ta yaya yankin arewa ya shiga cikin mummunan hali amma kun kasa fadawa gwamnati gaskiya? Idan ba za su iya ba shin ba zasu sauka daga mulkin ba, ko dole ne sai sun mulki jama’ah?

 

An yanka muna ‘yan uwa, kuma ace babu wata magana mai dadi? Har wani wawa zai fito yana ce muna wai talakawan da aka yanka, manoma masu neman abun da zasu ci su da iyalansu, wai basu nemi izinin gwamnati na yin noma a wurin da aka yi masu yankan rago ba?

 

Wallahi, wallahi, wallahi duk wani shege mun san shi, kuma mun san gidanshi. Na rantse da Allah zamu fara daukar mataki akan duk wani munafukin malami, da duk wani mayaudarin da ya sake fitowa ya yaudare mu!

 

Muna jira, Allah yasa mu sake jin wani wawan malami, ko wani wawan Dan siyasa, mara kishin al’ummarsa, ya fito da nufin ya yaudare mu. Wallahi sai mun hadu, mu da sauran talakawa, mun yi maganinsa, ko waye shi!

 

Wallahi, wallahi, wallahi muna kara fada maku cewa Hakurin mu ya kare. Mun gaji da wannan cin mutunci. Mun gaji, mun gaji, mun gaji!

 

Ku saurari abun da zai biyo baya In Shaa Allahu…

 

Daga karshe, ya ku ‘yan uwana ku sani, ni babu ruwana da ko wace jam’iyyah. Abun da ke faruwa a yankina na arewa, da kuma kasata Najeriya shine damuwa ta! Sannan ni ban damu da duk wani mai zagi na ba! Duk abunda zaka fada ka fada, ya rage naka. Ni dai Allah shine shaida na akan cewa na isar da sakon da ya kamata in isar. Kuma dukkanin mu zamu mutu mu tashi a gaban Allah, Mahaliccinmu, domin yayi muna hisabi!

 

Wassalamu Alaikum

 

Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here