NAHCON ta fara wayar da kai kan Adashin Gata na Hajji a Jihar Kogi

0
281

 

 

 

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), tare da haɗin gwiwar Jihar Kogi ta yi wani taro na wayar da kai ga masu ruwa da tsaki a kan sabon shirin nan na Adashin Gata na Hajji a ranar biyu ga watan Disamba a harabar hukumar da ke Lokoja.

 

Shugaban NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan, ya samu wakilcin jagoran tawogar, Imam Hassan Saad, wanda ya wakilci tawogar NAHCON ɗin da ta bankin Jaiz a taron.

 

A jawabinsa, Imam Saad ya yiwa mahalarta taron maraba ya kuma roƙe su da su jure su saurari maƙalar da Ishaq Ja’e zai gabatar a kan shirin Adashin Gata na Hajji domin tana da matuƙar muhimmanci.

 

A yayin gabatar da maƙalar, Ja’e ya faɗi duk abinda shirin ya ƙunsa da kuma alfanon sa.

 

Sauran jami’an bankin Jaiz kuma sun yi ƙarin haske a kan ɓangaren dabaru da fasaha na shirin.

 

A nashi jawabin, Shugaban Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Kogi, Sheikh Luqman Imam godewa jami’an NAHCON da na Jaiz yayi a bisa yin taron wayar da kan a jihar.

 

Ya kuma godewa mahalarta taron inda ya hore su da su kaiwa al’ummomin su saƙon abinda a ka tattauna a taron

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here