An yi gargaɗi kan takardar shaidar Ummara ta bogi

0
6

 

 

Ma’aikatar Kula da Harkokin Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta yi jan kunne a kan takardar shaidar Ummara ta bogi.

 

 

Wannan gargaɗi ya zo ne bayan da ma’aikatar ta gano wasu takardun shaidar zuwa Ummara na bogi da aka riƙa sayarwa da ƴan ƙasa da kuma baƙi.

 

 

Ma’aikatar ta gano cewa wasu ɓatagari ne suke buga takardun shaidar Ummara ɗin na bogi su riƙa damfarar maniyyata duba da irin tsananin buƙatar ta da ake yi inda wasu suke kwashe watanni ma basu samu ba, in ji kafar yaɗa labarai ta Al-Watan.

 

 

Babban Ofishi mai Lura da Masallatan Harami biyu masu alfarma ya gano cewa alhazan Ummara ne suka riƙa karɓar takardun na jabu, inda ta nuna takaicin cewa sun karɓi shaidar ne a hannun kamfanonin sufurin jiragen sama.

 

 

Ta manhajar Eatmarnah kaɗai a ka yarda alhazai da masu ziyarar Masallatan Harami guda biyu su tura buƙatar su ta zuwa.

 

 

Samun izinin yin ziyarar ƙabarin Ma’aiki mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da yin sallah a masallatan harami guda biyu yafi sauƙi.

 

 

Amma kuma da wahala maniyyaci ya samu iznin yin Ummara da kuma ziyarar ƙabarin Ma’aiki, wato raudha saboda tun a makonni da dama da suka gabata aka gama kame guraben neman zuwa Ummarar, shine ƴan damfara suka yi amfani da wannan damar suka riƙa damfarar alhazai ta hanyar sayar musu da takardar shaidar yin Ummara ta bogi.

 

 

Wannan ne ya sanya Saudiya ta gargaɗi ƴan ƙasa da kuma baƙi a kan zuwa wajen ɗaiɗai kun mutane ko kamfanoni da suke cewa suna sayar da takardar shaidar yin Ummara da ziyara zuwa ƙabarin Ma’aiki.

 

 

Ƙasar ta nanata cewa za a iya samun takardar a manhajar Eatmarnah ne kawai.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here