Hajji 2021: An samu ƙarancin maniyyata a Indiya saboda korona

0
410

 

 

Annobar COVID-19, wacce a ka fi sani da cutar korona ta sanya san samu ƙarancin maniyyatan Hajji 2021 a Ƙasar Indiya.

 

Mutane 3,200 ne kacal suka aika neman zuwa Hajjin 2021 daga garin Uttar Pradesh saɓanin mutanen 29,000 da suka aika neman zuwa ibadar.

 

A ranar 7 ga watan Nuwamba ne dai a ka buɗe hanyar aika neman zuwa ibadar ta yanar gizo da kuma ta amfani da takardu, inda a ranar 10 ga Disamba ne za a rufe karɓa.

 

Mahukunta sun alaƙanta ƙarancin maniyyatan na bana da annobar korona.

 

Haka kuma ba a samu mace ko ɗaya ta aika neman zuwa Hajjin a ƙarƙashin rukunin matan da za su je ba da muharrami ba.

 

A wannan rukunin, mata za su iya haɗuwa su biya su tafi Hajji, inda kwamitin tsare-tsaren Hajji na Indiya ya ware kujeru 500 domin irin waɗannan matan.

 

Sakataren Kwamitocin Hajji na Jihohi, Rahul Gupta ya bayyana cewa ƙasar na son tura adadin mahajjata mafi zuwa zuwa ƙasa mai tsarki amma wasu abubuwan ba a hannun hukumomi yake ba.

 

“Ba zamu iya cewa komai game da kason da aka fitarwa Uttar Pradesh ba saboda har yanzu muna jiran umarni ne,”

 

Ya amince da cewa korona na kawo illa ga mahajjata sannan kuma tuni yawan guraren aika neman zuwa Hajji a Uttar Pradesh ya ragu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here