Adashin Gata na Hajji: NAHCON ta fara shirin wayar da kai daga kudancin Nijeriya

0
302

 

 

 

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta fara shirin wayar da kai a kan Adashin Gata na Hajji da kudu maso yammacin ƙasarnan a Jihar Osun, inda za ta yi taron a ranar 14 ga Watan Disamba, 2020.

 

 

A tuna cewa a ranar 4 ga watan Oktoba, 2020 ne a ka ƙaddamar da shirin Adashin Gata na Hajji a Kano a bisa jagorancin Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

 

 

Saboda haka yayin da NAHCON ɗin ta ɗauki gaɓaran wayar da kan al’umma a kan manufofin shirin, za ta fara ne da jihar Osun a birnin Oshogo, Ekiti a Ado Ekiti da kuma Akure, Babban Birnin Ondo a ranar 14 ga watan da muke ciki.

 

 

Shi dai shirin Adashin Gata na Hajji wani sabon tsari ne na tara kuɗin zuwa aikin hajji da NAHCON da Hukumomin Hajji na Jihohi suka ƙirƙiro da haɗin gwiwa da bankin Jaiz.

 

 

Bayan sauƙi da tsarin zai samarwa maniyyata, sannan kuma zai bawa masu harkar hada-hadar hajji su samu sauƙin jigilar mahajjata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here