Sashen Yaɗa Labarai da Sadarwa na Babban Ofishin Kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya fara haɗa wani fim wanda zai nuna irin hoɓɓasar da Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu, Sarki Salman ya yi wajen daƙile yaɗuwar cutar korona a masallatan masu tsarki.
An tsara ɗaukar fim ɗin zai ɗauki awanni ɗari da hamsin.
Sultan Al-Masoudi, Babban Daraktan Sashin ya ce fim ɗin zai bayyana irin yanayin da Harami ya kasance lokacin ɓullar annobar da kuma irin hoɓɓasar da aka yi wajen kare alhazai da masallata ta hanyar amfani da ƙwararan matakan kariya.
Haka kuma fim ɗin zai nuna yadda aka kashe maƙudan kuɗaɗe da kuma amfani da fasahohin zamani da kawo ƙwararru wajen yiwa masallatan biyu hidima domin daƙile yaɗuwar annobar da ma sauran cututtuka.
“Tuni Babban Ofishin ya gama cimma yarjejeniya da ɗaya daga cikin gidajen jarida na ƙasa domin haɗa fim ɗin.
Haka kuma an kawo ƙwararrun ƴan jarida da za su haɗa gwiwa da sashin yaɗa labarai na babban ofishin domin samun nasara aikin,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa fim ɗin zai nuna kyakkyawan tsarin mulki da ƙwarewa wajen tsara cinkoson al’umma da yadda ta ke aiwatar da matakan kariya ta tsari ingantacce.
Al-Masoudi ya kuma bayyana cewa za a kwashe kwanaki goma ana ɗaukar fim ɗin a ciki da harabar masallatan haramin na tsawon awanni goma sha biyar a kowacce rana.
Ya ƙara da cewa ƙwararrun ma’aikata ne ƴan ƙasa da suke da cikakkiyar ƙwarewar aiki za su haɗa fim ɗin .