Hukumar Kula da Harkokin Alhazai Musulmai ta Jihar Taraba ta yi rashin jami’in alhazai na ƙaramar hukuma, Alhaji Babayo Umar.
A sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Hamza Baba Muri ya fitar, marigayi Umar ya rasu ne a tsakar daren jiya.
Ya ce kafin rasuwar sa, marigayin shine jami’in alhazai na ƙaramar hukumar Karim-Lamido kuma shine Sintalin masarautar tsohuwar Mutu.
Ya kuma sanar da cewa za a binne mamacin a yau da misalin ƙarfe 10 na safe.