Babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Bauchi ne ya bayyana haka.
Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi Karkashin Jagorancin Babban Sakataren Hukumar Alh. Abubakar Babangida Tafida (Tafidan Giade) tana sanar da Alhazan da sukayi aiki a shekarar 2019 cewa Gwamnatin jihar Bauchi Karkashin Jagorancin Sanata Bala A. Muhammad (Kauran Bauchi) ta bada umarnin biyansu kudeden su da aka samu wasu baraguribin ma’aikata sukayi sama da fadi da zunzurutun kuddi Naira #74,022,573 a cikin kudin da maniyyatan suka biya domin zuwa kasa Mai tsarki, an gano hakanne lokacin da aka samu ragin #51,000 akan kowani kujera da maniyyaci ya biya domin tafiya aikin hajji.
Babban Sakataren yayin zantawa da manema labarai
Ma’aikatan sunyi amfani da rasiti da hatimin boge ne wajen gudanar da wannan ta’annati, tunin Gwamnatin jihar Bauchi Karkashin Jagorancin Sanata Bala A Muhammad ta kafa kwamitin bincike kuma aka gano su aka gurfanar dasu gaban kuliya domin fuskantar Shari’a. Ganin halin da mahajjatan suka shiga tun a wancen lokacin yasa Mai girma Gwamnan jihar Bauchi ya bada umarnin biyansu kudeden Wanda nan take aka saka ranar Litinin 14/Disamba a matsayin ranar da za’a fara biyan wannan kuddi Wanda adadin alhazan yakai 1653.
Yadda tsarin biyan wannan kuddi zai kasance shine za’ayi abin Kashi uku ne:
Akwai Kwamitin da zasu biya a Ma’akatar Hukumai Alhazai ta jiha
Da kwamitin da zasu kasu Kashi uku
i. Bauchi ta Kudu
ii. Bauchi ta Arewa
iii. Bauchi ta Tsakiya
Abubuwan da ake bukata daga kowani Mahajjaci sune kamar Haka:
i. E-Passport
ii. Original Receipt
iii. Bank Taller
Wannan sune ake bukata azo dasu kuma za’a fara be daga ranar Litinin 14/12/2020 zuwa ranar Juma’a 18/12/2020.
Hikima Hausa TV