Bauchi za ta fara dawowa da alhazan 2019 ragowar kuɗaɗen su ran Litinin

0
8

 

 

Hukumar Alhazai Musulmai ta Jihar Bauchi ta ce ta kammala shirin maidowa da alhazan 2019 kuɗaɗen ragin da aka yi na kuɗin Hajji da kuma wasu hidmomi da suka biya amma ba a yi musu ba.

 

A wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Jami’in haɗa labarai na hukumar, Muhammad Sani Yunusa hukumar ta ce aiki biyan kuɗaɗen, wanda za a fara yin sa a ranar Litinin, 14 zuwa 17 ga watan Disamba da muke ciki, zai haɗa da dukkanin alhazan da suka je aikin hajji a 2019 a jihar.

 

Sanarwar ta ce “alhazan da suka biya kuɗin aikin Hajji kai tsaye ta hukumar da kuma waɗanda suka samu guraben zuwa ta gwamnati, za su karɓi kuɗaɗen su a ranar Litinin a sakatariyar hukumar. Su kuma alhazai daga ƙanan hukumomin Alƙaleri da Kirfi za su haɗu a Alƙalerin domin karɓar kuɗaɗen nasu,”

 

Su kuma alhazan da suka fito daga Darazo, Dambam da Misau za su karɓi nasu kuɗaɗen a Shalkwatar Sakatariyar Misau. Sauran kuma da suka fito daga Katagum za su karɓi nasu haƙƙoƙin a Shalkwatar Sakatariyar Azare duk a ranar.

 

A washe gari kuwa, ranar Talata kenan, 15 ga watan Disamba, alhazai daga Ƙanan Hukumomin Dass, Tafawa Ɓalewa da Bogoro su taru a  Bununu domin karɓar kuɗaɗen su. Su kuma waɗanda suka fito daga Ganjuwa, Warji da Ningi za su karɓi nasu a Ningin. Sannan waɗanda suka fito daga Ƙananan Hukumomin Zaki da Gamawa za su karɓa a shalkwatar Gamawa ɗin.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar Laraba, 16 ga Disamba, za a yi rabon kuɗin a Toro ga alhazan da suka fito daga Ƙaramar Hukumar Toron. Sai kuma waɗanda suka fito daga Jama’are da Itas-Gaɗau zasu karɓi nasu a Shalkwatar Sakatariyar Jama’are.

 

Za a kammala rabon ne a ranar Alhamis, 17 ga Disamba ga Alhazan Ƙaramar Hukumar Bauch a Shalkwatar Sakatariyar Bauchin, sai kuma Shira da Giaɗe a Shalkwatar Sakatariyar Shira ɗin.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkanin Alhazan da abin ya shafa za su zo da fasfunan su, shaidar biyan kuɗi ta banki da kuma rasitin biyan kuɗi kuma daidai ƙarfe 9 na safe ake so kowa ya hallara a wajen karɓar kuɗaɗen.

 

Sanarwar ta bayyana cewa ba a yarda a karɓi kuɗi ta ɗan aike ba, kowa sai dai ya zo da kan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here