Sama da mata miliyan ɗaya ne suka yi Ummara daga Oktoba

0
590

 

Babban Ofishin Kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya ce sama da mata miliyan ɗaya (1,000,000) ne suka yi ibadar Ummara da kuma yin sallah a babban masallacin tun daga lokacin da aka buɗe Ummara na daki-daki.

 

Zango na uku, wanda ya fara daga ɗaya ga watan Nuwamba ya bawa ƴan ƙasashen waje izinin yin ibadar tare da ƴan ƙasa.

 

Saudi Arebiya ce dai ta dakatar da yin Ummaraa watan Maris sannan ta takaita adadin mahajjata zuwa dubu goma a watan Yuli a wani mataki na daƙile annobar korona.

 

Mutane 84,000, da suka haɗa da mata 26,209 ne na rukunin farko da suka yi Ummara a lokacin kuma mutane 6,000 ne suke yin ibadar a rana.

 

Mutane 210,000 ne suka yi Ummara a zango na biyu tsawon makonni biyu a mataki na alhazai 15,000 a rana.

 

Sannan kuma mutane 500,000 ne suka yi ibadar Ummara a zango na uku.

 

Adadin mata 326,603 ne suka yi Ummara a zango na biyu da na uku, inda mata 669,818 ne suka samu damar yin sallah a babban .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here