Hukumar kula da Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Katsina ta ce ta kammala tsare-tsare na fara rijistar maniyyata na Hajjin 2021.
Shugaban hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ne yabayyana hakan a ranar Talata a yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce shirin ya zo ne sakamakon umarnin da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayar.
Kuki ya ce za a fara yin rijistar ne ta amfani da kuɗaɗen ajiya da maniyyatan Hajjin 2020 suka bayar.
Sabunta muku: Bai kamata gwamnati ta riƙa kashe kuɗaɗe don ɗaukar nauyin aikin Hajji ba- Sarkin Dutse
Sauran abubuwa kuma za su gudana ne daidai da tsare-tsaren da Hukumomin Saudi Arebiya suka bayar gami da adadin guraben alhazan da za a baiwa Nijeriya.
Ya kuma jaddada ƙudurin hukumar na yin rijistar a bisa tsarin duk wanda ya fara zuwa ya biya kuɗi, inda ya alƙawarta cewa za a bawa alhazan da suka biya kuɗaɗen su na Hajjin 2020 muhimmanci.
Shugaban ya yi bayanin cewa maniyyaci zai biya N500,000 ta banki a matsayin kuɗin ajiya, inda ya ƙara da cewa za a yi aikin rijistar ne a cibiyoyi bakwai a faɗin jihar.
Kuki ya kuma gargaɗi maniyyatan da su kula da duk sharuɗɗan yin rijistar domin gudun tafka kuskure a yayin yin rijista ɗin da zai iya haifar da soke kujerar su ta Hajji.