NA MUSAMMAN: Saudiya ta fara buga bizar Ummara ga ƴan Nijeriya

0
799

Hukumar Hajji ta Saudi Arebiya ta amince da ta fara buga buza ga alhazan Nijeriya da za su yi Ummara .

Wannan amincewar ta kuma nuna sahalewa ga kamfanonin jigilar Hajji da Ummara Masu Zaman Kansu da su fara yiwa maniyyatan rijista.

Samfurin bizar da aka fara yi bayan kullen korona, wanda aka wallafa a shafin Hajj Reporters na whatsapp, an baiwa Alhaji Naziru Rabiu Gambo, Shugaban Kamfanin Earth Travel & Tour Ltd.

A zantawar da ya yi da Hajj Reporters ɗin, Gambo ya tabbatar da sahihancin bizar da aka wallafa a IHR ɗin, inda ya tabbatar da cewa bizar, mai lamba 6072351265 sahihiya ce da Ofishin Jakadancin Saudiya na Kano ya tabbatar da sahihancin ta.

Haka kuma ya ƙara da cewa bizar tana da wa’adin kwanaki talatin ce.
 
Haka kuma Shugabar AL Khausa Travel, Haiya Rabi ta tabbatar da gaskiyar lamarin ga Hajj Reporters, inda ta ƙara da cewa an tabbatar da sahihancin bizar ta wani kamfani da ya samu yarjewar Hukumar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya.

Ta ce “dole sai kowanne kamfani ya samu mafi ƙarancin alhazai guda hamsin kuma su kasance a cikin rukuni,”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here