Nuna Halin Girma, Kyauta Da Karamci Irin Na Annabi Muhammad (SAW)!

0
853

Daga Imam Murtadha Gusau
Talata, 15/12/2020
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwa masu daraja, ku sani, duk duniya ta shaida cewa addinin Musulunci addini ne da ya kafu akan nuna halin girma, da alheri, da karamci, da kyauta, domin haka ne ma Allah Ta’ala ya siffanta Annabinsa (SAW) da cewa:

“Lallai ne, shi (Alkur’ani) tabbas maganar wani Manzo (Mala’ika Jibirilu) mai daraja ne. Kuma shi ba maganar wani mawaki ba ne. Kadan kwarai za ku gaskata.” [Suratul Hakkah, 40-41] 

Siffanta shi da Allah yayi da cewa mai karamci ne, wannan alama ce dake nuna girman kyawawan dabi’unsa, kuma wannan sanannen abu ne tun kafin ayi masa wahayi da yake kunshe da Manzanci.

Haka nan mai dakin Annabi Muhammad (SAW), wato Khadijah (RA), ta shaide shi akan wadannan kyawawan dabi’u na sa, kuma ta tabbatar masa da cewa, a sanadiyyar haka, Allah ba zai taba kunyata shi ba, ko ya dora makiyansa a kan sa, a inda take cewa:

“Lallai ne kai kana sadar da zumunci, kuma kana daukar nauyin marasa galihu, kana bai wa marasa shi, kuma kana saukar baki kayi masu hidima, kuma kana taimakon wadanda bala’i ya fada masu.” [Bukhari]

Wadannan dabi’u da ya tashi da su, babu shakka suna nuni da karamcinsa da kuma mika hannunsa ga mutane, da kyautarsa.

Kamar yadda Abdullahi Dan Abbas (RA) ya siffanta shi da cewa:

“Manzon Allah (SAW) shine mafi kyautar mutane, kuma kyautarshi tafi yawa a cikin watan Ramadan, a lokacin da Jibrilu yake ziyartarsa, ya kasance yana ziyartarsa a kowane dare na Ramadan, sai suyi nazarin Alkur’ani. Wallahi Manzon Allah yafi iska mai dauke da kyauta yawan kyauta.” [Bukhari]

Da zamu yi nazarin rayuwarsa bayan aiko shi da sakon Manzanci, zamu gani cewa a kullun yana kokari wurin kwadaitar da Sahabbansa da iyalansa wurin su yawaita karamci da kyauta, domin shine hanyar tsira da rabauta. Za mu ga haka yayin da ya fada wa Sahabbansa, da dukkanin al’ummarsa cewa:

“Babu wata rana da za’a wayi gari face akwai mala’iku biyu masu sauka daga sama, daya yana addu’a, yana cewa: “Ya Allah ka maye wa mai ciyarwa da alheri.” Dayan kuma yana cewa: “Ya Allah ka salwantar da dukiyar mai rowa da mako.” [Bukhari]

Wannan shine samfurin rayuwar Annabi Muhammad (SAW) a kowane lokaci. Yana ciyarwa, sannan yana umurni da yin haka, don haka ne ma Musulmi a wancan lokacin, suka yi rayuwa mai tsafta, suka zauna lafiya, suka buwayi makiyansu, karkashin wannan kyakkyawar koyarwa ta Manzon Allah (SAW). An ruwaito Hadisi daga Sahal dan Sa’ad yana cewa:

“Wata mata tazo wurin Manzon Allah (SAW) da wata irin riga mai kyawo, mai kama da malum-malum, sai tace ya Manzon Allah ina son in tufatar da kai wannan rigar, sai Manzon Allah (SAW) ya karba ya yafa ta.” Sai wani daga cikin Sahabbai ya gan shi da ita, sai yace ya Manzon Allah, wannan riga tana da kyau, don haka ka ba ni ita, sai Manzon Allah (SAW) yace: “Babu damuwa.” Yayin da Manzon Allah (SAW) ya bar wurin, sai Sahabbansa suka zargi mutumin, suka ce masa: “amma baka kyauta ba da ka amshi wannan rigar daga hannun Manzon Allah (SAW), kuma alhali ka sani, yana son ta, kuma ka san baya hanawa kuma baya cewa babu idan aka tambaye shi ko aka roke shi. Sai mutumin ya basu amsa da cewa: “Ai ba wani abu yasa na tambayeshi wannan rigar ba face neman samun albarka da tubarrakin jikinsa, domin tsammanin a binne ni cikinta idan na mutu.” A wata ruwayar kuma: “Sai kuwa wannan rigar ta kasance likkafani a gare shi bayan mutuwarsa.” [Bukhari]

A nan zamu kara fahimtar maganar Jabir (RA) da yake cewa:
“Ba’a taba tambayar Manzon Allah (SAW) wani abu ba yace a’a, ko yace babu.” [Bukhari]
Manzon Allah (SAW) ya kasance abun buga misali, kuma abun koyi wurin nuna halin girma, wato karamci da kyauta, domin kuwa a lokacin da dukiyar Bahrain tazo masa, duk da kasantuwarta mafi yawan dukiya da tazo masa, sai yace: “Ku rabar da ita a Masallaci.” [Bukhari]

Manzon Allah (SAW) ya kasance shine yake fara bayarwa ba sai an roke shi ba, kuma yana mai farin ciki da annashuwa da hakan, ba ya nuna bacin rai da damuwa, ko kuma yace ana matsa masa da roko ko tambaya, har yake cewa:

“Ba zan so in mallaki gwargwadon girman Dutsen Uhudu na zinare ba sannan kuma ace har kwanaki uku su zo su shude wannan zinare yana tare da ni (ba tare da na rabar da shi ba) koda kwatankwacin zinare daya kuwa. Sai dai dan abun da zai ragu don biyan bashi. Amma duka zan rabar da wannan zinarin. In bayar ta gaba, in bayar ta baya, kuma in bayar ta dama in bayar ta hagu.” [Bukhari] 

Bayar da kyauta da nuna halin girma, wato karamci, sun kasance dalili na Musuluntar da dama daga cikin Mushrikai, domin kuwa Annabi Muhammad (SAW), ya kasance yana yin kyauta irin ta wanda baya tsoron talauci. Anas dan Malik ya ruwaito cewa, ba’a taba tambayar Manzon Allah (SAW) wani abu game da sha’anin Musulunci ba face sai ya bayar da shi, sai wani mutum yazo wurinsa, sai ya bai wa wannan mutumin turken dabbobi cikin tsakanin duwatsu guda biyu (wato garke biyu na dabbobi), yayin da wannan mutumin ya koma wurin mutanensa, sai yace masu: yaku mutane na! Wallahi ku Musulunta, domin Muhammadu yana bayar da kyauta irin ta mutumin da baya tsoron talauci.”

Kuma nau’ukan karamcin Annabi Muhammad (SAW) suna da yawa, domin an karbo daga Rubayyi’u ‘yar mu’awwiz, Dan gafra’u tana cewa:

“Nazo wurin Manzon Allah da bangaji na dabino, sai ya bani cikin tafin hannunsa na kayan kawa da ado, ko kuma zinari, sai yace ma ta: “Kiyi kawa da ado da wannan.”

Wannan dalili ne da hujja da yake nuna kai wa makura a wurin karamcinsa, ta yadda yake kyautar da duk abin da yazo hannunsa, duk da cewa yana bukata. Bai mallaki komai ba na daga dukiya, har ta kai yana karbar kyauta ‘yar kadan shi kuma ya bayar da tukwici da babban abu, saboda halin girma.

Kamar yadda Annabi (SAW) ya kasance mai kiyayewa ne dukkan kiyayewa akan kyauta da karamci, har a lokacin da yake kan shimfidarsa ta mutuwa, ya kai kololuwa wurin kyauta wadda babu wani mutum cikin talikai da ya kai ta, har sai da Nana Aisha (RA) ta fada cewa: “Zafin ciwo ya tsananta ga Manzon Allah (SAW) a lokacin yana da dinarai bakwai ko tara, sai yace: “Ya Aisha: ina wadannan dinaran suke?” Sai tace: suna wuri na. Sai yace: “Ki yi sadaka dasu” ta ce: sai na shagalta da hidimarsa, sai ya sake cewa: “Ya Aisha, ina wadannan dinaran suke?” Sai tace, suna wuri na, sai yace: “kawo man su”, tace: sai na kawo mashi su, sai ya sanya su a tafin hannun shi sannan yace: “Menene tsammanin Muhammadu idan ya hadu da Allah, alhali wannan dukiya tana hannunshi?!” [Ibn Hibban]

Sannan sai Ummu Salamah ta shiga wurinsa tace: “Sai nayi zaton wannan maganar ta zafin ciwo ce, sai tace: ya Manzon Allah! Yaya na ga ranka a bace?” Sai yace: Saboda dinaran nan ne guda bakwai wadanda aka bamu su jiya, mun wuni dasu suna kunshe a karkashin makwanci na.” A wata ruwaya kuma: “An bamu su kuma ba mu kyautar da su ba.” [Ahmad]

Daga cikin mafi kyawon misalai wadanda zan rufe wannan bayani da su, na nuna halin girma da karamcin Annabi Muhammad (SAW), shine abun da ya faru ranar yakin Hunain, wanda yake nuna karamcinsa a fili, yayin da Musulmai suka samu ganima mai yawan gaske a wannan rana, wadda yawanta ya wuce lissafi. Kai har sai da mutanen kauye –kamar yadda Jubair Ibnu Mud’im yake cewa – suka takurawa Annabi (SAW) da roko da tambaya da naci, duk inda yasa kafarsa sai su bi shi suna rokonsa, har sai da yazo gindin wata katuwar bishiyar magarya, amma ba su kyale shi ba! Daga nan sai kaya ta kama mayafinsa. Sai yace: “Ku miko man mayafina, kuma da ace wannan ganyen bishiyar zai zama dabbobi da duk sai na rabar da su a tsakaninku! Kuma ba zaku same ni marowaci, ko marar cika alkawari, ko makaryaci ko matsoraci ba. [Bukhari]

Annabi Muhammad (SAW) bai tattare wadannan dukiyoyi ya hana wa sauran mutane ba. Bai yi rayuwa irin ta daga shi sai ‘ya ‘yansa ba, domin shi ba dukiya ce a gabansa ba. Annabi (SAW) yayi amfani da wannan dukiya don jawo hankalin manyan Kuraishawa zuwa ga Musulunci, kamar su Abu Sufyan, Shugaban Kuraishawa, da Hakim Ibnul Hizam, da Harith Ibnu Hisham Dan uwan Abu Jahal, da Nadhir Ibnul Harith Dan uwan Nadhar Ibnul Harith wanda ake yiwa lakabi da Shaidanin Kuraishawa, wanda ya kasance daga cikin manyan makiyan Annabi (SAW). Sannan kuma Annabi ya raba wannan dukiya ya bai wa shugabannin sauran kananan Kabilu, irinsu Uyainah Ibnu Hasan, Shugaban kabilar Banu Fazarah, da kuma Akra’a Dan Habis, Shugaban kabilar Banu Tamim. Kuma Annabi (SAW) ya kasance yana raba wannan dukiya ga talakawa, domin su samu karfi da nishadin bautawa Allah, Mahaliccinsu yadda ya kamata. Domin Annabi (SAW) yana sane da cewa, lallai talauci dan uwan kafirci ne. Sannan kuma yana sane da cewa, babu abun da talauci bai sa mutum ya aikata na barna! Sai wannan karamci da kyauta da halin girma da Manzon Allah (SAW) ya nuna masu ya zama shine turken da ya daure imani a cikin zukatansu.

Misali, ga abun da Anas (RA) yake fada game da irin halinsu:

 “Mutane da dama sun shiga addinin Musulunci don kwadayin samun duniya, amma daga bisani sai Musulunci ya zama mafi soyuwa a gare su fiye da duniya da abinda yake cikinta.” [Muslim]

Jama’ah, haka fa ya kamata Musulmi ya zama, haka ya kamata Musulmi ya rayu a duk halin da ya samu kan sa a ciki. Abun mamaki ne kwarai Musulmi ya kasance marowaci. Duk kuwa Musulmin da ya zama marowaci, to ya sani, yana daga cikin masu taimakawa wurin ruguzawa tare da rusa addinin Musulunci!
 
Ina Shugabannin mu, ina ‘Yan siyasar mu, ina Sarakunan mu, ina Malaman mu, ina ma’aikatan mu, ina jami’an tsaron mu, kai ko wane fannin mutum yake, yasan da sanin cewa, wallahi addinin Musulunci ba addini ne na marowata ba! Idan dai har da gaske kake yi, cewa kai kana cikin masoya Manzon tsira, Manzon Rahama, Fiyayyen halitta, Shugaba Annabi Muhammad (SAW), to ya zama tilas, kuma dole ka zamanto mai kyauta, mai nuna halin girma, kuma mai karamci!

Allah ya taimake mu, yasa mu dace, amin.
Wassalamu Alaikum
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun shi a lambar waya kamar haka: 08038289761.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here