Hajjin 2021: Kaduna za ta fara rijistar alhazai ran Litinin

0
267

 

Hukumar Kula da Jin daɗi da Walwalar Alhazai Musulmai

ta Jihar Kaduna ta ce za ta fara rijistar alhazan a ranar Litinin.

Wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Salisu Sani Anchau ya fitar ta ce Shugabar Hukumar ta Riƙon Ƙwarya, Hajiya Hannatu Zailani ce ta bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai.

Ta ce”Hukumar Kula da Jin Daɗi da Walwalar Alhazai Musulmai ta Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin fara karɓar kuɗaɗen ajiya ga maniyyata a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba,”

Ta ƙara da cewa maniyyatan za su biya kuɗin ajiyar ne daga Naira dubu ɗari takwas zuwa naira miliyan ɗaya da rabi kafin Hukumar Hajji ta Ƙasa ta faɗi iya adadin kuɗin da za biya.

Hajiya Hannatu ta yi kira ga maniyyata da su je ofishin hukumar mafi kusa da su, kuma su 5afi da fasfo ɗin su domin samun damar karɓar takardar biyan kuɗin.

Ta kuma yi kira ga al’umma da su yi amfani da damar shirin nan na Adashin Gata na Hajji da su riƙa ajiye kuɗaɗen kashi-kashi domin sauƙaƙa musu wajen biyan kuɗin zuwa Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here