Sanwo Olu zai ƙaddamar da Adashin Gata na Hajji a Legas

0
8

 

 

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo- Olu ya shirya tsaf domin ƙaddamar da shirin Adashin Gata na Hajji ga jihohin da ke yankin gudu maso yamma na Nijeriya.

 

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Shugaban Hukumar Kula da Jin daɗin Alhazai ta Jihar Legas, Rahman Ishola, za a yi taron ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, a Eko FM Marquee, titin Lateef Jakande a unguwar Agidingbi da ke Ikeja.

 

Malam Ishola ya nanata cewa shirin adashin, wanda yake na haɗin gwiwa ne tsakanin NAHCON, Hukumomin Hajji na Jihohi da kuma Bankin Jaiz, an ƙirkiro shi ne domin a sauƙaƙa da kuma cikawa masu ƙaramin ƙarfi burin su na zuwa aikin Hajji.

 

Ya kuma bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Legas ɗin, Dakta Kadri Obafemi Hamzat, zai halarci taron wanda zai kasance ƙarƙashin jagorancin Farfesa D. O. S Noibi, sannan Oba Saheed Ademola Elegushi na Lardin Ikate ne zai zama masarauci uban taro.

 

Sauran baƙin da ake sa ran za su halarci gagarumin taron sun haɗa da Shugaban NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan, Shugabannin Hukumomin Hajji na Jihohi a faɗin ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Hajji.

 

Ishola yayi kira ga waɗanda za su halarci taron da su zo da takunkumin fuska, inda yayi gargaɗin cewa duk wanda ba zai bi sharuɗɗan kariya daga cutar korona ba 5o ba za a bari ya halarci taron ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here