Mata 1,500 aka ɗauka domin yiwa alhazai mata hidima a Harami

0
505

 

 

Babban Ofishin Kula da Masallacin Harami da na Ma’aiki ya ɗauki mata 1,500 aiki domin hidimatawa alhazai mata da waɗanda za su kawo ziyara zuwa masallacin mai girma.

 

Daga cikin mata 1,500 ɗin, 600 daga sashin ayyukan fasaha da gudanarwa na Babban Ofishin suke.

 

50 daga ciki su za su riƙa tuƙa motoci masu amfani da wutar lantarki, 850 kuma daga Sashin Cigaban Mata na ofishin suke.

 

Kashi hamsin daga cikin matan da aka ɗauka aikin za su yi aiki ne a fannin gudanarwa da hidimatawa da kuma ɓangaren kula da ƙofofi da ɓangaren kura da sufuri, goge na ƙasa da kuma shimfiɗu sai kuma kula da ruwan zamzam.

 

Sauran kuma za a rarraba su zuwa sashe-sahse da suka haɗa da sashin gudanar da bada shawarwari da gindaya sharuɗɗa, sashin kimiyya da fasaha, sashin ababan tarihi da ilimi, sai kuma babban sashe na gudanarwa da dabaru, sadarwa da yaɗa labarai da sauran ayyukan masallacin.

 

 

Mataimakiyar Shugaban Babban Ofishin,  Dr. Al-Anoud bint Khalid Al-Aboud ta tabbatar da cewa wannan tsarin na cikin tsare-tsaren da za a yiwa Ofishin nan da shekarar 2024, wanda yake da ƙudurin ƙara bunƙasa hidimar da ake yiwa Masallatai biyun masu tsarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here