An dakatar da Ummara ga ƴan ƙasashen waje

0
474

 

 

 

A ranar Litinin ne dai Saudi Arebiya ta sanar da dakatar da jigilar jirage zuwa ƙasashen waje na tsawon mako ɗaya.

 

Saudiyan ta ce ta dauki matakin ne a matsayin kariya daga yaɗuwar sabon nau’in cutar korona wacce ke yaɗuwa a Britaniya da kuma sauran ƙasashen nahiyar Turai.

 

Yayin da a ka dakatar da tashi da saukar jirage zuwa ko daga ƙasashen waje, matakin ya nuna cewa suma alhazan Ummara ba za a samu damar jigilar su zuwa ƙasar ba.

 

Wannan shine karo na biyu da aka dakatar da sufurin jirgin sama a Saudiya bayan an ɗage dakatarwar farko a watan jiya.

 

Har yanzu dai Hukumar Hajji da Ummara ba ta yi bayani ba a hukumance game da dakatarwar da kuma masaukin baƙi alhazai da abin ya rutsa da su.

 

Ita kuma Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta bayyana cewa dakatarwar da aka yiwa ɓangaren sufurin jiragen sama ta wucin gadi ce tsawon mako ɗaya amma da yiwuwar a ƙara mako ɗaya bayan Hukumar Lafiya ta Ƙasar ta yi nazari a kan yanayin.

 

Amma kuma Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan ta bawa jiragen ƙasashen waje da matakin ya rutsa da su lokacin da suke ƙasar da su koma ƙasashen su.

 

A sani cewa Saudiya ce ke da mafi ƙarancin waɗanda suka kamu da korona a halin yanzu a yankin su bayan da yawan kamuwa dan cutar yake raguwa a kowacce rana.

 

Wannan matakin dai ya bada mamaki bayan da Saudiya ɗin ke shirin cigaba da harkar jigilar jiragen sama kamar yadda aka saba daga 1 ga watan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here