Hajjin 2021 zai zamto mafi tsada a Pakistan- Minista

0
712

Ministan kula da Harkokin Addini da Samar da Haɗin kai tsakanin Mabiya Aadinai a Pakistan, Pir Noor Ul Haq Qadri ya bayyana cewa Hajjin 2021 zai zamto mafi tsada sakamakon ƙirƙiro da tsarin Hanyoyin Aiwatarwa na Haƙiƙa (SOPs).

Ministan ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Litinin bayan ya halarci taro kan Hajji tare da Wakilan Ƙungiyar masu Gudanar da Harkokin Hajji na Pakistan da kuma ta Sindh a sansanin alhazai.
Ya bayyana cewa Hanyoyin Aiwatarwa na Haƙiƙa a kan korona ne za su sanya Hajjin na 2021 ya zamto mafi tsada. Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na nan tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan aiwatar da tsarin mulki kan Hajji na  2021 kuma suna duba yiwuwar samar da kayayyakin aiki ga alhazai a baɗi da kuma samar musu da rigakafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here