Ministan Harkokin Hajji da Ummara na Saudi Arebiya, Dakta Mohammed Saleh Benten ya bayyana cewa alhazai miliyan biyar ne suka yi Ummara tun bayan da aka buɗe cigaba da ummarar bayan an dakatar da ita sakamakon annobar korona, wacce aka fi sani da COVID-19.
Ministan ya bayyana cewa ba a samu rahoton mutum ɗaya da ya kamu da cutar korona ba a cikin alhazai da masallata, in jishi a wata ganawa da yayi da gwamnan Makkah, Khaled Al-Faisal a Jidda ranar Laraba.