Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) ta fara shirye-shiryen haɗin gwiwa da Jami’ar Ummul-Qura da ke Makka, Saudi Arebiya a kan ilimin gudanar da aikin Hajji.
Idan haɗin-gwiwar ya tabbata, ɗaliban da suke yin karatun fannin sanin makamar gudanar da aikin Hajji da ɗaukacin ayyukan ibada da ke cikin Hajji za su je Jami’ar ta Ummul-Qura da ke Makka su ƙarasa karatun a can.
Farfesa Muhammad-Bello Uthman, Babban Daraktan Cibiyar Ilimin Shari’ah ta Addinin Musulunci (CLIS), wanda da bayyana batun a Babban Taron Alƙalai na Shekara da ake yi a Zariya, ya kuma bayyana cewa jami’ar ta rattaba hannu a yarjejeniya da wasu jami’o’i guda biyu na ƙasashen waje a kan bincike a kan sanin ilimin yadda ake gudanar da ibada (fiƙhu), koyarwa da kuma musayar malamai da ɗalibai.
Farfesa Bello ya ƙara da cewa tun a farkon shekarar nan ne wata tawoga daga ABU ta ziyarci Ummul-Qura ɗin sannan ta gana da shugaban jami’ar ta yadda za a haɗa gwiwa a kan harkokin jigilar aikin Hajji da kuma ibadun da ake yi a lokacin aikin Hajjin.
“A ƙarƙashin yarjejeniyar, ɗaliban ABU zasu tafi Saudi Arebiya su kammala karatun nasu a jami’ar Ummul-Qura ɗin domin su ga yadda a ke gudanar da ibadar hajji a yayin da ake yin aikin Hajjin”
Digirin na biyu a Fannin Kasuwanci (MBA) da kuma ƙwarewa ta musamman a Ilimin Gudanar da Jigilar Aikin Hajji, wanda tuni Hukumar Kula da Harkokin Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta sahale a riƙa yin sa, na ƙarƙashin karatuttukan da ake yi daga gida a ƙarƙashin ABU.
Jami’ar, a wani talla da ta wallafa, ta yi kira ga masu sha’awa da su shiga shafin ta na yanar gizo www.apply.abudlc.edu.ng domin neman shiga shirin.
Ta kuma jaddada cewa duk mai sha’awa sai ya cika ƙa’idoji da kuma sakamakon karatu da ake buƙata da aka wallafa a shafin www.abudlc.edu.ng
Bayanin tallan ya bayyana cewa ɗibai za su riƙa samun rubutattun lakcoci da gubdarin kwasa-kwasai da za a yi a kan sabon karatun na tsawon awanni 24.