An ƙaddamar da shafin gudanar da Hajji ta internet da kati mai na’ura

0
856

 

 

 

Ma’aikatar Harakokin Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta ƙaddamar da sabon shafin gudanar da Hajji ta internet da kuma kati mai na’ura a ranar Asabar.

 

An ƙaddamar da shafin da kuma katin ne domin a gudanar da harkokin Hajjin ta baiɗaya daga dukkan masu ruwa da tsaki a ƙarƙashin ma’aikatar.

 

Za a bawa kowanne alhaji kati mai na’urar wanda yake dauke da bayanan alhaji, bayanan lafiya da kuma gurin zama.

 

Haka kuma katin zai taimakawa alhazai gurin gano masaukin su yayin da suke guraren ibada, sannan kuma zai riƙa nuna yadda za a ziyarci guraren ibadar da sauran ma gurare, da kuma uwa uba zai daƙile matsalar ɓullar alhazan bogi.

 

Wannan sabon tsarin na ɗaya daga cikin tsarurruka da ƙasar ke shirin ɓullo da shi a wani taron nuna al’adun gargajiya da a ka yi a Makka.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here