Hajjin 2021: IHR ta shawarci NAHCON kan yiwa maniyyata rijista daidai da ƙa’idojin korona

0
17

 

 

Ƙungiyar Masu Rahoto kan Hajji da Ummara, wacce a ka fi sani da Independent Hajj Reporters (IHR) ta yi kira ga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta ƙirƙiro da wasu ƙa’idoji da za su yi daidai da na kariya daga kamuwa da cutar korona a yayin rijistar maniyyata na Hajjin 2021.

 

Ƙungiyar ta bada shawarar ne a wata sanarwa da ta yi mai ɗauke da sa hannu na haɗin gwiwa da Shugaban ta na ƙasa, Ibrahim Muhammed da kuma Jam’in yaɗa labaran ta na ƙasa,  Abubakar Mahmoud a ranar Lahadi a Abuja.

 

Ƙungiyar ta ce shawarar ta zama wajibi duba da cewa Saudi Arebiya na bibiyar yadda ƙasashe a faɗin duniya ke yiwa maniyyata rijista domin ta tantance wacce ƙasa ya kamata ta bawa izinin zuwa Hajji ko kuma wacce bata cancanta ba.

 

Saboda haka IHR ɗin na son NAHCON da ta fitar da wani sahihin tsari wajen yin rijistar maniyyatan, wanda zai zo daidai da yadda Saudiya ta tsara a kan yin rijista bisa kan bin ƙa’idojin korona.

 

“Mun fahimci cewa hukumomin Hajji na jihohi na yin rijistar maniyyatan ne ta amfani da tsare-tsaren Hajji 2019 ba tare da canjawa zuwa tsare-tsaren da Hukumar Lafiya ta Saudiya ta fitar lokacin ummarar bana.

 

“Mun kuma fahimci cewa hukumomin Hajji na jihohi na maida hankali ne kawai kan biyan kuɗin ajiya da kuma karɓar fasuna da kuma hana biyan kuɗin ta ɗan aike.

 

“A yayin cutar korona ta ke kawo naƙasu ga aikin hajji, ya kamata NAHCON da hukumomin Hajji na jihohi su ɗauki Hajjin 2021 a matsayin wani tushe na kawo tsare-tsare kan yin rijista ta hanyar bin ƙa’idojin korona da suka haɗa da cancanta, ƙayyade shekaru, lafiya, nagarta a yayin yin rijista ɗin”

 

IHR ɗin ta yi nuni da cewa idan hukumomin Hajji na jihohi suka yi rijistar maniyyata ba tare da duba da tsare-tsaren kariya kan korona ba to hakan ka iya kawo naƙasu a Hajjin 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here