Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON da kuma Kwamitin Shugaban Ƙasa na Yaƙi da Korona, PTF, da ma Hukumar Lafiya ta Ƙasa sun fara fitar da wasu matakai na kariya daga annobar COVID-19, wato korona a yayi jigilar aikin Hajji.
Shugabar Sashin Hulɗa da Jama’a ta NAHCON ɗin, Fatima Sanda Usara ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar.
Usara ta ce an ɗauki matakin ne domin daƙile yaɗuwar cutar musamman bayan da zango na biyu na annobar ya kunno kai.
Ta ƙara da cewa NAHCON na jiran wasu matakan da Saudi Arebiya za ta fitar domin yin biyayya ga nauyin da take da shi na tsare-tsaren Hajji da kuma hidima da masallatai guda biyu masu tsarki.
“Hukumar za ta ci gaba da yabawa Saudiya a bisa mataki mai wahala da ta ɗauka domin daɗaɗawa al’ummar musulmi a faɗin duniya, musamman ma duba da cewa ba lallai ne a son ran ƙasar ta ɗauki matakan ba,”
Usara ta kuma ƙara da cewa da zarar ta karɓi bayanai daga Saudiya a kan sababbin matakai kan Hajjin 2021 da kuma ummara, to za ta ɗauki wasu matakai da suka dace domin amfanin alhazan Nijeriya.