Ummara: Alhazai 3 sun rasu bayan da motar su ta yi karo da rakumi

0
400

 

 

A ƙalla mutane uku ne aka rawaito cewa sun rasu bayan da motar bos mai ɗauke da alhazan Ummara 16 ƴan Ƙasar Egypt ta yi karo da raƙumi a Saudi Arebiya, in ji Ma’aikatar Harkokin Waje ta Egypt ɗin.

 

Hatsarin ya faru ne a wajen kilomita 310 daga garin Tabuka, wanda yake a arewa maso yammacin Saudiya yayin da Alhazan ke kan hanyar su ta zuwa Makka domin yin Ummara, inji Mataimakin Ministan Ƴan ƙasar Egypt da ke zama a kasashen waje a wata sanarwa da ya fitar.

 

“Ofishin Jakadancin Egypt na Jidda ya bibiyi lamarin matuƙa kuma yana tuntuɓar mahukunta a Saudiyya domin shirye-shiryen dawo da  zuwa ƙasar su da kuma bincika sanadiyyar hatsarin,” in jishi.

 

Mutane 3 ne dai suka rasu ana kawo su asibiti, inda mutane 13 suka samu raunuka daban-daban kuma suna karɓar magani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here