Saudi za ta janye dakatarwar da ta yiwa harkar sufuri ran 31 ga wata

0
946

Za ta buɗe dukkanin jigilar jiragen na ƙasashen waje

Saudi Arebiya ta amince da ɗage duk wani takunkumi na harkar sufuri da ta saka na wucingadi, inda za ta dawo da harkar sufurin jirgin sama na ƙasashen waje, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya rawaito a ranar Juma’a, inda yace a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Ministan Harkokin Cikin Gida ya samu bayanin.

An sake sabunta muku: Saudi za ta janye dakatarwar da ta yiwa harkar sufuri ran 31 ga wata

Matakin, wanda zai fara aiki tuƙuru daga ranar 31 ga watan Maris ya ƙunshi ƙa’idoji kamar haka.

Za a bar ƴan ƙasa su yi tafiya har zuwa wajen ƙasar sannan su dawo.

2- Za a ɗage dagatarwar wucingadi a harkar sufurin jirgin sama na ƙasashen waje.

3-Za a buɗe dukkanin iyakokin ƙasar na sama, Za a aiwatar da wannan matakin ne daidai da ƙa’idoji da sharuɗɗan da hukumomin da suka dace suka gindaya da kuma matakan kariya daga yaɗuwar cutar korona a faɗin ƙasar, inji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here