Rukunin farko na alhazan Ummara 75 a Nijeriya ya tashi zuwa Saudiya

0
785

Rukunin farko na alhazan Ummara a Nijeriya waɗanda za su yi ibadar Ummara tun bayan da aka dakatar da ibadar sakamakon annobar korona, ya tashi zuwa Saudiya.

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bayyana cewa adadin alhazai 75 ne suka tashi zuwa ƙasa mai tsarki aranar Talata.

Nasiha gareku: Hajjin 2021: IHR ta shawarci NAHCON kan yiwa maniyyata rijista daidai da ƙa idojin korona

NAHCON, a wani rahoto daga sashen yaɗa labarai na hukumar, ta ce akhazai 50 sun tafi ne ta kamfanin sufuri na Eminista Travels and Tours, inda sauran 25 ɗin kuma suka tashi ta kamfanin Earth Travels.

Shugaban sashen hidima na NAHCON, reshen Abuja, Umar M. Kalgo ya bayyana cewa Alhazan sun tashi ne daga filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Tafiyar ta Alhazan ta zama manuniya cewa an fara yin ibadar Ummara sannan kuma ana sa ran Saudi Arebiya za ta bari a je aikin Hajji bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here