YANZU-YANZU: Ƴan Nijeriya sun sauka a Jidda domin yin aikin Ummara

0
665

A safiyar yau Laraba ne dai rukunin farko na alhazai daga Nijeriya ya sauka a filin jirgin sama na King Abdulaziz dake Jidda domin yin aikin Ummara.

A jiya Talata ne alhazan, su 75 suka tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe.

Sune ayari na farko da suka je Saudiya domin yin Ummara tun bayan da aka buɗe yin Ummara ɗin bayan an dakatar da ita sakamakon annobar COVID-19.

Shawara a gare ku: COVID-19: Masu harkar Hajji da Ummara na tsananin buƙatar tallafi

NAHCON, a wani rahoto daga sashen yaɗa labarai na hukumar, ta ce akhazai 50 sun tafi ne ta kamfanin sufuri na Eminista Travels and Tours, inda sauran 25 ɗin kuma suka tashi ta kamfanin Earth Travels.

HAJJ REPORTERS ta fahimci cewa a halin yanzu alhazan na kan hanyar su ta zuwa Madina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here