Shugaban Mahajjata na Sakkwato ya bukaci jami’in rajistar da ya himmatu

0
1237

IHR

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai na Sakkwato, Alh, Mukhtari Bello Maigona ya bukaci jami’an rajistar alhazai a jihar su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu don tabbatar da nasara a lokacin aikin Hajjin 2021.

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Yakubu Ayuba ta ce “Alh Maigona ya yi kiran ne yayin ganawa da mataimakan jami’an rajistar alhazai.

A cewarsa, an shirya taron ne don tantance shirye-shirye a cikin kananan hukumomi 23 na LG da nufin magance duk wani kalubale da ka iya kawo cikas ga aikin Hajji 2021.

A yayin ziyarar, Darakta Janar na hukumar Alh, Shehu Dange ya bayyana matsayin rajistar mahajjata a jihar sannan kuma ya ce jihar ta shirya tsaf don shirin Aikin Hajji.

Taron ya samu halartar Daraktoci da wasu jami’an Hukumar da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here