Ummara: Alhazan Nijeriya 3 na ɗauke da COVID-19 a Saudiyya

    0
    496

     

     

    Gwaji ya nuna cewa uku daga cikin alhazai 75 da suka tafi Saudi Arebiya daga Nijeriya domin aikin Ummara na ɗauke da cutar korona, wacce aka fi sani da COVID-19.

     

    Jaridar yanar gizo ce ta rawaito wannan labarin a ranar Lahadi.

    YANZU-YANZU: Ƴan Nijeriya sun sauka a Jidda domin yin aikin Ummara

    Su dai alhazan na Nijeriya sun tashi ne a makon da ya gabata daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja domin yin Ummara.

     

    Daga cikin matakan kariya da ake ɗauka ya haɗa da killace maniyyata na kwanaki uku, daga bisani kuma sai a yi musu gwajin cutar korona kafin su fara ibadar Ummara.

     

    Bayan an yi gwajin ne, kamar yadda rahotanni suka bayyana a safiyar yau, shine sai a ka ga alhazan uku na Nijeriya na ɗauke da cutar.

     

    Rahotanni sun bayyana cewa tuni dai aka fara kulawa da alhazan uku da suka kamu da annobar.

     

    Sauran kuma da ba sa ɗauke da cutar tuni suka fara ziyara zuwa gurare masu tsarki a ɓangare na rukunnan ummarar. Daga bisani kuma sai su wuce Makka a gobe daga miƙati domin kammala aikin Ummarar.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here