NAHCON ta nemi haɗin kan Saudiya wajen baiwa sahihan kamfanunuwa damar bada bizar Ummara

  0
  406

  Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, Barista Zikrullah Kunle Hassan ya nemi haɗin kan Ƙasar Saudi Arebiya wajen bada izinin yin bizar Ummara ga sahihan kamfanunuwa waɗanda suke da sababbin takardun sahalewa kaɗai.

  A wata sanarwa da Shugabar Sashin Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Asabar, shugaban yayi wannan kira ne yayin da ya kai ziyara ta musamman ga sabon ambasadan Saudiyya a Nijeriya, Faisal Al-Ghamdi a ofishin sa da ke Abuja, babban birnin Nijeriya.

  Sanarwar ta ce Barista Hassan, wanda ya samu rakiyar Kwamishinan sa na ɓangaren gudanarwa, Alhaji Magaji Harɗawa, ya nemi taimakon Saudiya ɗin wajen daƙile harƙallar da wasu kamfanunuwa marasa lasisi je yi wajen kai mutane Saudiya ba tare da bisa ba a wani yanayi na fakewa da aikin Hajji ko Ummara.

  Shi kuwa ambasadan ya tabbatar da cewa kamfanunuwa da suke da sahihan takardu da aka tantance su kuma aka ɗora su a runbun ajiye bayanai na Ummara na yanar gizo na ƙasar Saudiyya ne kaɗai za su samu damar yin biza.

  Wannan roƙon da NAHCON ɗin ta yi ne ya sanya a ranar 25 ga watan Janairu ta fitar da sunayen sahihan kamfanunuwa 170 a jaridun ƙasar nan, inda ta kuma bayyana cewa wasu kamfanunuwan masu harkar Hajji da Ummara ɗin na ta zuwa suna yin rijista ana kuma tantance su kuma suma za a buga sunayen su a jarida idan an kammala tantancewar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here