Saudi Arebiya ta sanar da dakatar da sufurin jiragen sama daga ƙasashe ashirin daga ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu, ƙarfe 9 na yamma.
Sanarwa da ƙasar ta fitar ta ce dakatarwar ta faru ne a kan ƙasashen da aka samu ɓullar sabon nau’in cutar COVID-19.
Matakin, in ji sanarwar, ya haɗa da UAE, Jamus, Amurka, Indonesiya, Italiya, Pakistan, Brazil, Ingila, Turkiyya, Afrika ta Kudu, Faransa, Lebanon, Masar, Indiya da Japan.