Ministan Hajji da Ummara na Saudi Arebiya, Dr. Muhammad Saleh Benten, a ranar Alhamis ya bayyana cewa ƙasar ta maida alhazan Ummara ƴan ƙasashen waje 700,000, waɗanda suke Makka da Madina a lokacin ɓarkewar COVID-19 a farkon shekarar 2020.
“Lokacin da annobar ta ɓarke, akwai alhazan ummara 600,000 a makka da kuma 100,000 a Madina, lamarin da ya janyo aka rufe masallatai biyu masu tsarki,”
Benten ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayani a kan nasarorin da ƙasar ta samu a kan yaƙi da annobar da kuma yadda ta shafi Hajji da Ummara yayin taron kimiyya kan Hajji da Ummara da kuma ziyara ta bincike karo na 20.
Taron, mai taken bunƙasar tafiyar baƙin Allah zuwa ƙasa mai tsarki, wanda Jami’ar Ummul Qura ta gudanar.
Benten ya ƙara da cewa Saudiya ta samu nasarar daƙile annobar ne sakamakon zage dantse da ta yi wajen taimakawa al’ummar musulmi da kuma waɗanda suke da sha’awar zuwa ƙasar, inda ya yi godiya ga Allah da kuma ƙwazon da gwamnati tayi da kungiyoyi masu zaman kan su.
A kan batun aikin Hajji, Benten ya ce hukumar ta haɗa gwiwa da hukumomin da suka dace domin ƙirƙirar wasu tsare-tsare na aiwatarwa da kuma duba a kan ƙoƙarin ta a Hajjin da ya gabata musamman wajen tafiyar da tsarin cinkoson al’umma da kuma tabbatar da kariyar mahajjata.