Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa (EFCC) ta ƙwace SR miliyan 3.1, kimanin naira miliyan 315 a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, inda tayi awon gaba da mutane biyu da ke da alaƙa da kuɗaɗen.
An rawaito cewa an ƙunshi kuɗaɗen ne a cikin ambulan sannan aka totse su a cikin jakar nan ta matafiya mai suna ‘Ghana must go’ daga Saudi Arebiya zuwa Nijeriya ta jirgin Ethiopia.
DA ƊUMI-ƊUMI: Saudiya ta dakatar da sufurin jiragen sama daga ƙasashe 20
Jaridar Premium Times ce ta kawo labarin, inda ta ce itama ta samu labarin ne daga wata majiya ce daga EFCC ɗin, wacce ta nemi a sakaye sunan ta saboda bana bata umarnin yin magana ba.
Majiyar ta bayyana cewa tun ranar Litinin jami’an Hukumar Hana Fasa-ƙauri ta kama waɗanda ake zargi ɗin tare da kuɗaɗen.
Majiyar ta ce a wajen awon jakankuna ne jami’an Hukumar Hana Fasa-ƙauri su ka gano kuɗaɗen bayan da aka ƙetaro da su zuwa ƙasar nan a cikin jirgin Ethiopia.
Da yake tabbatar da kamen, Kakakin EFCC ɗin na ƙasa, Wilson Uwujaren ya ce waɗanda ake zargin suna bada gamsassun bayanai yayin da ake tuhumar su.