IHR ta yi kira da a riƙa kyautata hidimar alhazai

0
363

Ƙungiyar Masu Rahoto kan Hajji da Ummara, wacce aka fi sani da Independent Hajj Reporters (IHR) tayi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar Hajji da su tabbatar da cewa alhazai suna gamsuwa da kuɗaɗen da suke biya na aikin Hajji.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Ibrahim Muhammad ne yayi kiran yayin da ya ja tawogar ƴan ƙungiyar zuwa ziyara ta musamman ga Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Barista Zikrullah Kunle Hassan, ranar Alhamis a Abuja.

Muhammad ya ce IHR, wacce take ƙungiya mai zaman kanta a da take sa ido da rahototanni domin bunƙasa harkar aikin Hajji za ta ci gaba da yunƙuro wajen kawo tsare-tsare masu inganci, ya ƙara da cewa ” sai dai kuma masu ruwa da tsaki a Hajji ba sa ganin irin ƙwazon da muke yi,”

“Irin wannan dama yana faruwa, amma mu babbar buƙatar mu shine alhazai su riƙa ganin amfanin kuɗaɗen da suke biya,”

Shugaban ya ƙara da cewa, IHR, wacce take dandali ne na dukkanin ƴan jarida musulmai da suke da sha’awar bada gudunmawa a kan wayar da kan alhazai ɓangaren Hajji, tana kuma da alhakin sanya ido a harkar Hajji da Ummara.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar na da alhakin kawo sauyi a yanayin yaɗa labarai kan Hajji da Ummara da kuma canji kan tsare-tsaren Hajji ta hanyar bada sharhi da suka mai ma’ana.

” Sannan muna ɗora alhakin a kan masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa alhazai suna ganin amfanin kuɗaɗen da suke biya da kuma ƙirƙirar da dandali ta yin muhawara mai ma’ana wanda yake taimakawa wajen yin harkar aikin Hajji ba tare da matsala ba a Nigeria,”

A nashi ɓangaren, Hassan ya nuna cewa harkar Hajji fanni ne da ya ke buƙatar jajircewa da sa ido a ɓangaren yaɗa labarai zuwa ga al’umma.

Ya ce babbar buƙatar NAHCON itace ta mai matuƙar sauƙi ta yadda da kazo hukumar za ka samu biyan buƙata ba tare da wahala ba.

Ya ce NAHCON ta samu nasarori wajen kawo sauyi masu amfani a harkar Hajji a ƙasa.

Ya kuma ƙara da cewa NAHCON ta ƙirƙiro da Adashin Gata na Hajji, wanda aka fi sani da Hajji Savings Scheme domin bawa ƴan ƙasa masu ƙaramin ƙarfi damar tara kuɗaɗen zuwa aikin Hajji.

Shugaban ya daɗa da cewa Cibiyar Horaswa kan Aikin Hajji da ake shirin samar da ita za ta bunƙasa harkokin Hajji ga masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here