Ma’aikatar Harkokin Addini ta Saudi Arebiya ta buɗe masallatai 44 da ta rufe sakamakon ƙaruwar annobar COVID-19 a ƙasar.
An buɗe masallatan ne bayan an musu feshin magani na ciki da bai.
EFCC ta ƙwace kuɗaɗen Saudiya kimanin naira miliyan 315 a filin jirgin sama na Abuja
An ta cigaba da rufe masallatai, manyan kantuna, kasuwanni da guraren shaƙatawa a Saudiyya sakamakon ƙaruwar kamuwa da cutar korona a kasar.
A baya dai ministan ya bayyana cewar ana rufe masallatan ne na wucingadi kuma babu wata-wata za a cigaba da rufe su muddin al’umma suka ci gaba da ƙin bin matakan kariya daga kamuwa daga cutar korona ba, inda hakan har ya haifar da sake ƙaruwar kamuwa da ita.”