Gwamnan Makkah, Mai-martaba Yarima Badr bin Sultan ya gana da Muƙaddashin Ministan Hajji da Ummara a kan shirye-shiryen Hajjin bana.
IHR ta yi kira da a riƙa kyautata hidimar alhazai
Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya rawaito cewa shugabannin sun gana ne a kan shirye-shiryen Hajjin bana da kuma Ummarar Azumin watan Ramadana mai ƙaratowa.
A yayin ganawar ta su, sun tattauna kan muhimman batutuwa dangane da tsare-tsare da kuma shirye-shirye na musamman da za a yiwa alhazai baƙin Allah.