NA MUSAMMAN: Ran 18 ga Febrairu Ƴan Nijeriya 25 za su tashi zuwa Saudiya domin yin Ummara

0
3

Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na New Crescent Travel da haɗin gwiwar Raudah Travels And Tours Ltd sun shirya tsaf domin kwasar alhazan Ummara 25 daga Nijeriya zuwa Saudi Arebiya domin yin Ummara.

Alhazan Ummara ɗin za su tashi ne ranar 18 ga watan Fabrairu, ta jirgin Ethiopia daga filin tashi da saukar jiragen sama da ke Jihar Legas.

Babban Daraktan Raudah Travels And Tours Ltd, Alh Umar Abdulhadi Alfuti ya gayawa Hajj Reporters cewa kamfanin sa, da haɗin gwiwar New Crescent Tour sun kammala shirye-shirye kuma da yardar Allah, a ranar 18 ga Febrairu za su tashi daga Nijeriya zuwa Filin Tashi da Sauka na King Abdulaziz dake Jidda.

A nata ɓangaren, Babbar Daraktan New Crescent Travel, Sogbesan Hasanat Taiwo ta bayyana cewa tana yiwa maniyyatan fatan alheri da kuma addu’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here