DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Nijeriya 23 da suka tafi aikin Ummara sun sauka a Madina

0
1

Ƴan Nijeriya 23 da suka tafi yin ibadar Ummara zuwa Saudi Arebiya sun sauka a birnin Madina bayan da suka tashi daga filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammad dake birnin Ikko.

Hukumar Hajji a Kaduna ta ƙirƙiro da shirin jigilar alhazai kan tsarin COVID-19

Alhazan, waɗanda suka tafi a jirgin Ethiopia, sun sauka a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na King Abdul Aziz, inda jim kaɗan a ka kwashe su a mota zuwa Madina bayan sun kammala tantancewar lafiya da sauran takardu na tafiya.

A halin yanzu, alhazan na masaukin su a Madina inda za su kwashe kwanaki uku na killacewa kamar yadda dokar ƙasar ta tanada.

Independent Hajj Reporters ta rawaito cewa Alhazan sun tashi ne daga filin jirgin sama na Murtala Muhammad a ranar Alhamis ta jirgin Ethiopia mai lamba ET 2402.

Shugaban kamfanin Raudah Travels And Tours Ltd, Alh Umar Abdulhadi Alfuti ya shaidawa HAJJ REPORTERS cewa kamfanin nasa, da haɗin gwiwar New Crescent Tour, mallakar SOGBESAN HASANAT TAIWO sun yi dukkan tsare-tsare ta yadda alhazan za su yi aikin Ummara ba tare da wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here