Hukumar Kula da Walwala da Ji daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta ƙirƙiro da wani tsari na baiɗaya a kan COVID-19 wanda zai mata jagora da ma’aikatan ta wajen aiwatar da hada-hadar aikin Hajji.
Tun farko dai Shugabar hukumar, Hajiya Hannatu Zailani, a shekarar 2020 ta baiwa Daraktan Gudanarwa, Mallam Abubakar Alhassan da ya kafa kwamitin ƙwararru da za su zauna su yi bincike domin gano wani tsari da za a yi amfani da shi wajen hada-hadar aikin Hajji ta bana tare da duba da yadda za a kare alhazai da ma’aikatan hukumar daga kamuwa da cutar korona.
Tsarin, wanda zai kasance daidai da yardajjen tsari na bakiɗaya da masu ruwa da tsaki a aikin hajji suka ɓullo da shi, bai samu tabbatuwa ba sakamakon soke aikin Hajjin 2020 da aka yi.
Amma saboda ƙaruwar annobar a faɗin duniya, sai kwamitin ya cigaba da aiwatar da umarnin da aka bashi, inda tuni ya kammala aiki, wanda ake sa ran zai zamto jagora a hada-hadar aikin Hajji 2021 da hukumar za ta yi.
Shirin zai kasance nagartacce wajen kare alhazai da kuma ma’aikatan hukumar yayin aikin Hajji.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Mallam Abubakar Hassan, ya yi aiki ne da wasu ƙwararru daga waje a fannin lafiya wajen yin garambawul ɗin ɗaukacin hada-hadar aikin Hajji na Kaduna domin ya yi daidai da na ƙasa domin ta cimma buƙatar ta na yin aikin Hajji lafiya lau ba tare da matsaloli ba.
Nan ba da daɗewa ba kwamitin zai miƙa kundin tsarin ga kwamitin kar ta kwana kan COVID-19 na Jihar Kaduna.
Haka kuma hukumar za ta raba kundin tsarin ga Hukumomin Kula da Jindadi da Walwalar Alhazai na ƙasa domin taimaka musu wajen aiwatar da aikin su.
Hukumar ta ce duk hukumar Hajjin da take da buƙata sai ta tuntuɓi Independent Hajj Reporters domin samun kundin na yanar gizo.